Monday 1 December 2025 - 23:16
Ya Zama Wajibi Makaratun Ilmin Addinin Musulunci (Hauza) Su Kasance a Matakin Duniya

Hauza/ Shugaban Hauzar Khurasan, ya yin jaddada mahimmancin kasancewar Hauza zuwa ga matakin duniya, ya bayyana rawar da irin wadannan cibiyoyin ke takawa wajen isar da saƙon Musulunci da juyin juya halin Musulunci ga al’ummar duniya a matsayin wani abu mai muhimmanci. Ya kuma bayyana kokari da hazakar cibiyar Hauzar Khurasan a kan wannan tafarki.

Hujjatul Islam Wal Muslimin Ali Khayyat, Shugaban Makarantun Ilimin Addinin Musulunci (Hauza) na Khurasan, a yayin tafiyarsa zuwa ƙasar Iraki don halartar taron duniya kan Mawallafi Allama Mirza Na’ini (RA), a cikin wata hira da wakilin ofishin dillancin labaran Hauza, ya bayyana wajabcin kasancewar makarantun ilimin addinin Musulunci a matakin duniya, yana mai cewa: “Makarantun ilimin addinin Musulunci (Hauza) suna da wani aiki da aka ba su wanda shi ne aikin yaɗa sakon Musuluncin; aiki ne na duniya wanda bai iyakance ga wata kabila, jama’a ko birni ba. Don haka, kasancewar makarantun na ilimin addinin Musulunci (Hauza) zuwa ga matakin duniya, wani abu ne wajibi kuma tabbatacce.”

Ya kara da cewa: “Saƙon Musulunci, saƙo ne mai jan hankali kuma na duniya wanda yake jan hankali ga dukan ’yanci da mutanen da suka ’yantar da kansu daga ƙulli, waɗanda suke a cikin ɗaurin fiɗirarsu. Bugu da ƙari, saƙon juyin juya halin Musulunci wanda aka tsara shi daga tsantsar Musulunci, a yau ya zama abin lura a duniya, kuma na tabbatar cewa wannan saƙon yana da ƙarfi sosai wajen jawo hankalin al’ummar duniya.”

Kwarewar Ilimin Cibiyar Ilimin Addinin Musulunci ta Khurasan

Shugaban Hauzar Khurasan, yana mai nuni ga ƙarfin cikin gida na wannan cibiya, ya ce: "Hauzar Khurasan na ɗaya daga cikin cibiyoyin da ke da ƙarfin ilimi da kuma manyan ƙwararru. Dalibai da yawa sun san yarukan ƙasashen waje, kuma akwai cibiyoyin ilimi masu aiki da tasiri a cikin wannan cibiya waɗanda suke gudanar da ayyuka masu muhimmanci. Wannan ƙarfin zai iya zama tushen fadada tasirin makarantun ilimin addinin Musulunci a matakin duniya."

Hujjatul Islam Khayyat a ƙarshe ya jaddada cewa: "Yin amfani da wannan ƙarfin da kuma yin hulɗa da zata amfanar tare da cibiyoyi da majalisai na ilimi na duniya, zasu iya taimakawa wajen cika aikin makarantun ilimin addinin Musulunci a duniya fiye da yadda yake a yanzu."

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha